• بسم اللّٰه الذي لا يضر مع اسمه شيء في الأرض ولا في السماء وهو السميع العليم
    Bismillahilladhi la yadurru ma'a ismihi shay'un fil-ardi wa la fis-sama'i wa huwa as sami'ul-'alim.

    Manzon Allah (ﷺ )yace: "Duk wanda ya fadi wannan addu’a sau uku da safe da yamma, babu wani abu da zai cutar dashi ."
    بسم اللّٰه الذي لا يضر مع اسمه شيء في الأرض ولا في السماء وهو السميع العليم Bismillahilladhi la yadurru ma'a ismihi shay'un fil-ardi wa la fis-sama'i wa huwa as sami'ul-'alim. Manzon Allah (ﷺ )yace: "Duk wanda ya fadi wannan addu’a sau uku da safe da yamma, babu wani abu da zai cutar dashi ."
    Love
    1
    0 Commentaires 0 Parts 165 Vue 0 Avis
  • Wasu suna kunyar yaɗa al'amuran Addini ta wayoyinsa, sun manta da cewa aikin Annabawa ne, don haka babu wani aiki da ya kai shi daraja Allah ya mana taimako
    Wasu suna kunyar yaɗa al'amuran Addini ta wayoyinsa, sun manta da cewa aikin Annabawa ne, don haka babu wani aiki da ya kai shi daraja Allah ya mana taimako
    Love
    1
    0 Commentaires 0 Parts 167 Vue 0 Avis
  • ƴn ƙananun sana'oin nan naku na mata a gida akwai albarka acikinsu!
    Ku fadada tunani, ku kalli location naku.
    Ku kawo abunda aka fi buƙata
    Ku jure! Kuyi addua! kuyi haƙuri! ku gwada zaku yimun addua

    ZANCHEN HIKIMA 🍇
    ƴn ƙananun sana'oin nan naku na mata a gida akwai albarka acikinsu! Ku fadada tunani, ku kalli location naku. Ku kawo abunda aka fi buƙata Ku jure! Kuyi addua! kuyi haƙuri! ku gwada zaku yimun addua ZANCHEN HIKIMA 🍇
    Love
    1
    0 Commentaires 0 Parts 645 Vue 0 Avis
  • "Kuma Ubangijinka yana halitta abin da yake so, kuma yana zaɓa. Zaɓi bai kasance a gare su ba".
    [Suratul Qasas Aya: 68].

    Abin baƙin ciki sai kaga mutane da dama suna shishigi cikin al'amuran da Allah bai bada ikon zaɓi a cikinsu ba:

    Namiji yana jin haushin mace saboda duka ƴaƴan da take haifa mishi mata ne! Shin dama tana da zaɓi cikin abin da Allah zai halitta?

    Masu kushe halittar ƴan'uwansu, wannan ya cika baƙi, wannan tsawonshi yayi yawa, wannan gajere, Shin kuna da iko ne gurin zaɓan yadda Allah yaso su kasance?

    Har yanzu baki yi aure ba!
    Har yanzu baki haihu ba!
    Ya aka yi aurenki ya mutu!
    Ya aka yi kika kamu da ciwon nan!

    Shin dama mutum shi yake zaɓan kaddarar shi?

    Ku ji tsoron Allah ku iya bakinku cikin abubuwan da bawa ba shi da zaɓi akan su.

    *Oum Hanan* 🌹
    "Kuma Ubangijinka yana halitta abin da yake so, kuma yana zaɓa. Zaɓi bai kasance a gare su ba". [Suratul Qasas Aya: 68]. Abin baƙin ciki sai kaga mutane da dama suna shishigi cikin al'amuran da Allah bai bada ikon zaɓi a cikinsu ba: Namiji yana jin haushin mace saboda duka ƴaƴan da take haifa mishi mata ne! Shin dama tana da zaɓi cikin abin da Allah zai halitta? Masu kushe halittar ƴan'uwansu, wannan ya cika baƙi, wannan tsawonshi yayi yawa, wannan gajere, Shin kuna da iko ne gurin zaɓan yadda Allah yaso su kasance? Har yanzu baki yi aure ba! Har yanzu baki haihu ba! Ya aka yi aurenki ya mutu! Ya aka yi kika kamu da ciwon nan! Shin dama mutum shi yake zaɓan kaddarar shi? Ku ji tsoron Allah ku iya bakinku cikin abubuwan da bawa ba shi da zaɓi akan su. *Oum Hanan* 🌹
    Love
    1
    0 Commentaires 0 Parts 206 Vue 0 Avis
  • Imam Ash-Shaukany Allah yayi masa rahma ya ce:

    "Daga cikin mafi girman Zikrori akwai azhkar ɗin safiya da maraice waɗanda suka tabbata daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

    Domin lallai akwai amfani mai girma a cikinsu, da kuma samun garkuwa daga sharrori.

    Saboda haka duk wanda yake son tsira daga musibun duniya da kuma dacewa da alkhairan duniya da lahira, to ya lizimci waɗannan azhkar ɗin kuma ya dinga yin su a kowace safiya da maraice.
    [📚قطر الولي].


    *Oum Hanan* 🌹
    Imam Ash-Shaukany Allah yayi masa rahma ya ce: "Daga cikin mafi girman Zikrori akwai azhkar ɗin safiya da maraice waɗanda suka tabbata daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Domin lallai akwai amfani mai girma a cikinsu, da kuma samun garkuwa daga sharrori. Saboda haka duk wanda yake son tsira daga musibun duniya da kuma dacewa da alkhairan duniya da lahira, to ya lizimci waɗannan azhkar ɗin kuma ya dinga yin su a kowace safiya da maraice. [📚قطر الولي]. *Oum Hanan* 🌹
    Love
    1
    0 Commentaires 0 Parts 168 Vue 0 Avis
  • *ASSALAMU ALAIKUM BARKAN MU DA SAFIYAR YAU [TALATA]*

    *NASIHAR MU TA YAU*
    ```Idan kanaso ka gama lafiya kada ka yarda ka dauki kazafi a matsayin makamin fada wallahi tunda aka halicchi duniya babu wanda yayi sharri ya cimma nasara, kada mu zama sai mun 6ata wani saboda kawai mu tsarkake kan mu.

    *Ya ALLAH ka tsaremu yiwa wani kazafi kada muyi kar Ayimana Amin ya Allahu.*
    *ASSALAMU ALAIKUM BARKAN MU DA SAFIYAR YAU [TALATA]* *NASIHAR MU TA YAU* ```Idan kanaso ka gama lafiya kada ka yarda ka dauki kazafi a matsayin makamin fada wallahi tunda aka halicchi duniya babu wanda yayi sharri ya cimma nasara, kada mu zama sai mun 6ata wani saboda kawai mu tsarkake kan mu. *Ya ALLAH ka tsaremu yiwa wani kazafi kada muyi kar Ayimana Amin ya Allahu.*
    Love
    1
    0 Commentaires 0 Parts 159 Vue 0 Avis
  • *MAFARIN TAFIYA*
    (Yaƙin Ma'aurata)

    Ina yawan samun koke-koken sabbin ma'aurata game da yawan saɓani ko rashin jituwa da suke samu da abokan rayuwarsu a farkon zama.

    Abin da nake so masu shirin aure da ma'aurata su fahimta:
    Wannan saɓanin da yake yawan faruwa a shekarar farko na aure, ba yana nufin auren ba zai yuwu ba ne, kuma ba yana nufin ma'auratan sun gaza ba ne, kusan dole ne a samu hakan ga mutane biyu da suka fara rayuwa tare a inuwa ɗaya, alhali sun fito daga rassa daban-daban; wataƙila al'adunsu ya banbanta, yanayin inda suka taso, tarbiyyarsu, ko ma yarensu.

    Kuma duk lokacin da mutum biyu suka zauna tare ko da kuwa abota ce ko ƙawance to dole sai an yi haƙuri da juna.

    Duk da cewa lokacin neman aure ana tattaunawa domin a fahimci juna, amma maganar gaskiya:
    Baza ku san juna cikakken sani ba, sai kun zauna tare.

    Saboda haka kafin ku kai ga matakin fahimtar juna, dole ne duka ɓangarorin biyu ku rungumi haƙuri, ku bi komai sannu sannu a hankali.

    Nasihata gare ku itace:
    Ku kasance masu hikmah:
    Musamman namiji, tunda kai ne jagora, ka san yadda zaka tafiyar da saɓani cikin lumana da hikmah ba tare da zargi ko tashin hankali ba.

    Don Allah maza:
    Ku kasance masu haƙuri da ƙura-kuren da kuke gani, kuyi gyara cikin nasiha da taushin harshe.

    Mata:
    Ku kasance masu buɗaɗɗiyar zuciya wajen karɓan gyara, namijin da yake so ki samu babban matsayi a zuciyarsa, shi ne wanda zai dinga miki gyara yana ɗaura ki a hanya, domin idan ƙura-kurenki suka yi yawa ba tare da gyara ba matsayinki zai iya zagwanyewa a zuciyarshi.

    Kuma ku sani:
    Waɗanda kuke gani sunyi nasara a aurensu, ba wai don basa saɓani ba ne; a'a sun kasance masu juriya ne gurin fuskantar matsalolinsu, masu ƙoƙarin fahimtar juna, da kuma kyautata wa juna zato.

    Don Allah, ku ɗauki wannan shekarar ta farko a matsayin "Shekarar haƙuri" kada kuyi saurin yanke wa juna hukunci a cikinta, saboda muhimmancin haƙuri a zaman aure ya sanya bayan anyi aure (a cikin al'ummar Hausawa) kullum dangin ango da na amarya addu'ar su ita ce Allah ya bada zaman haƙuri, saboda haka matuƙar al'amari bai taɓa imani da lafiyar jiki ba ko afkawa haramun to haƙuri da addu'a da kawar da kai zasu magance dukkan matsaloli.

    Billah alaikum:
    Ku kyautata niyyoyinku, ku zauna da juna da zuciya ɗaya.

    Allah ya ƙarfafe ku, ya sanya albarka a cikin zamantakewarku, ya kare ku daga ko wace irin fitna.

    *Oum Hanan* 🌹
    *MAFARIN TAFIYA* (Yaƙin Ma'aurata) Ina yawan samun koke-koken sabbin ma'aurata game da yawan saɓani ko rashin jituwa da suke samu da abokan rayuwarsu a farkon zama. Abin da nake so masu shirin aure da ma'aurata su fahimta: Wannan saɓanin da yake yawan faruwa a shekarar farko na aure, ba yana nufin auren ba zai yuwu ba ne, kuma ba yana nufin ma'auratan sun gaza ba ne, kusan dole ne a samu hakan ga mutane biyu da suka fara rayuwa tare a inuwa ɗaya, alhali sun fito daga rassa daban-daban; wataƙila al'adunsu ya banbanta, yanayin inda suka taso, tarbiyyarsu, ko ma yarensu. Kuma duk lokacin da mutum biyu suka zauna tare ko da kuwa abota ce ko ƙawance to dole sai an yi haƙuri da juna. Duk da cewa lokacin neman aure ana tattaunawa domin a fahimci juna, amma maganar gaskiya: Baza ku san juna cikakken sani ba, sai kun zauna tare. Saboda haka kafin ku kai ga matakin fahimtar juna, dole ne duka ɓangarorin biyu ku rungumi haƙuri, ku bi komai sannu sannu a hankali. Nasihata gare ku itace: Ku kasance masu hikmah: Musamman namiji, tunda kai ne jagora, ka san yadda zaka tafiyar da saɓani cikin lumana da hikmah ba tare da zargi ko tashin hankali ba. Don Allah maza: Ku kasance masu haƙuri da ƙura-kuren da kuke gani, kuyi gyara cikin nasiha da taushin harshe. Mata: Ku kasance masu buɗaɗɗiyar zuciya wajen karɓan gyara, namijin da yake so ki samu babban matsayi a zuciyarsa, shi ne wanda zai dinga miki gyara yana ɗaura ki a hanya, domin idan ƙura-kurenki suka yi yawa ba tare da gyara ba matsayinki zai iya zagwanyewa a zuciyarshi. Kuma ku sani: Waɗanda kuke gani sunyi nasara a aurensu, ba wai don basa saɓani ba ne; a'a sun kasance masu juriya ne gurin fuskantar matsalolinsu, masu ƙoƙarin fahimtar juna, da kuma kyautata wa juna zato. Don Allah, ku ɗauki wannan shekarar ta farko a matsayin "Shekarar haƙuri" kada kuyi saurin yanke wa juna hukunci a cikinta, saboda muhimmancin haƙuri a zaman aure ya sanya bayan anyi aure (a cikin al'ummar Hausawa) kullum dangin ango da na amarya addu'ar su ita ce Allah ya bada zaman haƙuri, saboda haka matuƙar al'amari bai taɓa imani da lafiyar jiki ba ko afkawa haramun to haƙuri da addu'a da kawar da kai zasu magance dukkan matsaloli. Billah alaikum: Ku kyautata niyyoyinku, ku zauna da juna da zuciya ɗaya. Allah ya ƙarfafe ku, ya sanya albarka a cikin zamantakewarku, ya kare ku daga ko wace irin fitna. *Oum Hanan* 🌹
    Love
    2
    0 Commentaires 0 Parts 633 Vue 0 Avis
  • A RIƘE FALAƘI DA NASI

    1. LOKACIN BACCI

    2. BAYAN SALLOLIN FARILLA

    A CIKIN ZIKIRIN SAFE DA YAMMA.

    DOMIN TSARI DAGA MUGAYE NA FILI DA NA ƁOYE.
    A RIƘE FALAƘI DA NASI 1. LOKACIN BACCI 2. BAYAN SALLOLIN FARILLA A CIKIN ZIKIRIN SAFE DA YAMMA. DOMIN TSARI DAGA MUGAYE NA FILI DA NA ƁOYE.
    Love
    2
    0 Commentaires 0 Parts 221 Vue 0 Avis
  • "Wallahi babu wanda yake jinka a jikin shi sai wanda yake sonka"

    Abu Ɗalha ya cewa Ummu Sulaim:
    Lallai naji sautin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yayi rauni, kuma na tabbata sanadiyyar yunwa ne, shin ko kin rage wani abu?
    [Bukhari ne ya ruwaito shi].


    Duk wanda yake sonka soyayya ta gaskiya yana jinka a cikin jikinshi, yana fahimtar halin da kake ciki ba tare da kayi magana ba, yana jin sautin zuciyarka ko da baya kusa da kai.

    Allah ya haɗa mu da masoya na gaskiya ya tashe mu a ƙarƙashin inuwar al-arshinSa Subhanahu🤍.

    *Oum Hanan*
    "Wallahi babu wanda yake jinka a jikin shi sai wanda yake sonka" Abu Ɗalha ya cewa Ummu Sulaim: Lallai naji sautin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yayi rauni, kuma na tabbata sanadiyyar yunwa ne, shin ko kin rage wani abu? [Bukhari ne ya ruwaito shi]. Duk wanda yake sonka soyayya ta gaskiya yana jinka a cikin jikinshi, yana fahimtar halin da kake ciki ba tare da kayi magana ba, yana jin sautin zuciyarka ko da baya kusa da kai. Allah ya haɗa mu da masoya na gaskiya ya tashe mu a ƙarƙashin inuwar al-arshinSa Subhanahu🤍. *Oum Hanan*
    Love
    2
    0 Commentaires 0 Parts 206 Vue 0 Avis
  • *ƊIYA MACE ƳAR GATA*!
    🌸😍🌸

    Idan tana ƴa:
    Tana buɗewa mahaifinta ƙofofin Aljannah: Manzon Allah ﷺ ya ce:
    "Duk wanda ya kasance yana da ƴaƴa mata guda uku, ko ƴan uwa mata guda uku, yaji tsoron Allah mai Girma da Buwaya ya tsayu a kansu (wurin tarbiyyantar dasu), zai kasance tare da ni a Aljannah kamar haka! sai yayi nuni da yatsunsa guda biyu"
    [Ahmad ne ya ruwaito shi].


    Idan tayi aure:
    Tana cika rabin addinin mijinta:
    Manzon Allah ﷺ ya ce:
    "Idan bawan Allah yayi aure, toh tabbas ya kama hanyar cika rabin addini, saboda haka ya ji tsoron Allah game da sauran rabin da ya rage".
    [صحيح الجامع].


    Idan ta zama uwa:
    Aljannah tana ƙarƙashin kafawuwanta:
    "Wani mutum yazo gurin Annabi ﷺ sai ya ce: Ya Manzon Allah, Wane ne a cikin mutane yafi cancanta in kyautata mishi gurin zamantakewa da mu'amala? Sai Annabi ﷺ yace: "mahaifiyarka" sai ya sake tambayarsa yace sai wa? Sai Annabi ﷺ yace "Mahaifiyarka" sai ya kara tambayar Annabi ﷺ sai wa? Sai Annabi ﷺ ya ce "Mahaifiyarka" sai ya sake tambayarsa yace sai wa? Sai Annabi ﷺ yace sannan sai "Mahaifinka".
    [Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi].

    *Haƙiƙa mace tana da babban matsayi a musulunci*!
    *Alhamdu-Lillahi Ala Ni'imatil Islaam*

    *Oum Hanan* 🌹
    *ƊIYA MACE ƳAR GATA*! 🌸😍🌸 Idan tana ƴa: Tana buɗewa mahaifinta ƙofofin Aljannah: Manzon Allah ﷺ ya ce: "Duk wanda ya kasance yana da ƴaƴa mata guda uku, ko ƴan uwa mata guda uku, yaji tsoron Allah mai Girma da Buwaya ya tsayu a kansu (wurin tarbiyyantar dasu), zai kasance tare da ni a Aljannah kamar haka! sai yayi nuni da yatsunsa guda biyu" [Ahmad ne ya ruwaito shi]. Idan tayi aure: Tana cika rabin addinin mijinta: Manzon Allah ﷺ ya ce: "Idan bawan Allah yayi aure, toh tabbas ya kama hanyar cika rabin addini, saboda haka ya ji tsoron Allah game da sauran rabin da ya rage". [صحيح الجامع]. Idan ta zama uwa: Aljannah tana ƙarƙashin kafawuwanta: "Wani mutum yazo gurin Annabi ﷺ sai ya ce: Ya Manzon Allah, Wane ne a cikin mutane yafi cancanta in kyautata mishi gurin zamantakewa da mu'amala? Sai Annabi ﷺ yace: "mahaifiyarka" sai ya sake tambayarsa yace sai wa? Sai Annabi ﷺ yace "Mahaifiyarka" sai ya kara tambayar Annabi ﷺ sai wa? Sai Annabi ﷺ ya ce "Mahaifiyarka" sai ya sake tambayarsa yace sai wa? Sai Annabi ﷺ yace sannan sai "Mahaifinka". [Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi]. *Haƙiƙa mace tana da babban matsayi a musulunci*! *Alhamdu-Lillahi Ala Ni'imatil Islaam* *Oum Hanan* 🌹
    Love
    2
    0 Commentaires 0 Parts 226 Vue 0 Avis
Zoomer Africa https://zoomer.africa