*ƊIYA MACE ƳAR GATA*!
🌸😍🌸

Idan tana ƴa:
Tana buɗewa mahaifinta ƙofofin Aljannah: Manzon Allah ﷺ ya ce:
"Duk wanda ya kasance yana da ƴaƴa mata guda uku, ko ƴan uwa mata guda uku, yaji tsoron Allah mai Girma da Buwaya ya tsayu a kansu (wurin tarbiyyantar dasu), zai kasance tare da ni a Aljannah kamar haka! sai yayi nuni da yatsunsa guda biyu"
[Ahmad ne ya ruwaito shi].


Idan tayi aure:
Tana cika rabin addinin mijinta:
Manzon Allah ﷺ ya ce:
"Idan bawan Allah yayi aure, toh tabbas ya kama hanyar cika rabin addini, saboda haka ya ji tsoron Allah game da sauran rabin da ya rage".
[صحيح الجامع].


Idan ta zama uwa:
Aljannah tana ƙarƙashin kafawuwanta:
"Wani mutum yazo gurin Annabi ﷺ sai ya ce: Ya Manzon Allah, Wane ne a cikin mutane yafi cancanta in kyautata mishi gurin zamantakewa da mu'amala? Sai Annabi ﷺ yace: "mahaifiyarka" sai ya sake tambayarsa yace sai wa? Sai Annabi ﷺ yace "Mahaifiyarka" sai ya kara tambayar Annabi ﷺ sai wa? Sai Annabi ﷺ ya ce "Mahaifiyarka" sai ya sake tambayarsa yace sai wa? Sai Annabi ﷺ yace sannan sai "Mahaifinka".
[Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi].

*Haƙiƙa mace tana da babban matsayi a musulunci*!
*Alhamdu-Lillahi Ala Ni'imatil Islaam*

*Oum Hanan* 🌹
*ƊIYA MACE ƳAR GATA*! 🌸😍🌸 Idan tana ƴa: Tana buɗewa mahaifinta ƙofofin Aljannah: Manzon Allah ﷺ ya ce: "Duk wanda ya kasance yana da ƴaƴa mata guda uku, ko ƴan uwa mata guda uku, yaji tsoron Allah mai Girma da Buwaya ya tsayu a kansu (wurin tarbiyyantar dasu), zai kasance tare da ni a Aljannah kamar haka! sai yayi nuni da yatsunsa guda biyu" [Ahmad ne ya ruwaito shi]. Idan tayi aure: Tana cika rabin addinin mijinta: Manzon Allah ﷺ ya ce: "Idan bawan Allah yayi aure, toh tabbas ya kama hanyar cika rabin addini, saboda haka ya ji tsoron Allah game da sauran rabin da ya rage". [صحيح الجامع]. Idan ta zama uwa: Aljannah tana ƙarƙashin kafawuwanta: "Wani mutum yazo gurin Annabi ﷺ sai ya ce: Ya Manzon Allah, Wane ne a cikin mutane yafi cancanta in kyautata mishi gurin zamantakewa da mu'amala? Sai Annabi ﷺ yace: "mahaifiyarka" sai ya sake tambayarsa yace sai wa? Sai Annabi ﷺ yace "Mahaifiyarka" sai ya kara tambayar Annabi ﷺ sai wa? Sai Annabi ﷺ ya ce "Mahaifiyarka" sai ya sake tambayarsa yace sai wa? Sai Annabi ﷺ yace sannan sai "Mahaifinka". [Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi]. *Haƙiƙa mace tana da babban matsayi a musulunci*! *Alhamdu-Lillahi Ala Ni'imatil Islaam* *Oum Hanan* 🌹
Love
2
0 Comments 0 Shares 230 Views 0 Reviews
Zoomer Africa https://zoomer.africa