*Muhimmancin Karatun Alƙur’ani a Watan Ramadan.*

*Ramadan wata ne da aka saukar da Alƙur’ani a cikinsa, kamar yadda Allah Ya ce:*
*“Watan Ramadan wanda aka saukar da Alƙur’ani a cikinsa, shiriya ga mutane…” (Al-Baqarah: 185). Wannan ya sa karatunsa a wannan wata ya fi lada da tasiri a zuciya sama da sauran watanni.*

*Manzon Allah ﷺ ya kasance yana ƙara yawaita karatun Alƙur’ani a Ramadan, har ma Mala’ika Jibrilu (AS) yana yi masa muraja'a da Alƙur'ani a kowane dare. Wannan yana nuna muhimmancin komawa ga Alƙur’ani domin tsarkake zuciya, da ƙarfafa imani, da neman kusanci da Allah.*

*Karatun Alƙur’ani a Ramadan:*
• *Yana ƙara haske da nutsuwa a zuciya.*
• *Yana ninka lada, domin wata ne na alheri da rahama.*
• *Yana taimaka wa mai azumi ya kiyaye harshensa da halayensa.*

*Don haka, ya dace mu tsara lokaci a Ramadan domin yawaita karatu da tadabburi da sauraren tafsirai daga bakin malamai, da aiki da Alƙur’ani, domin shi ne babban sakon wannan wata mai alfarma.*

_©By Zauren Hikimomin Malaman Sunnah🖋️_
*Muhimmancin Karatun Alƙur’ani a Watan Ramadan.* *Ramadan wata ne da aka saukar da Alƙur’ani a cikinsa, kamar yadda Allah Ya ce:* *“Watan Ramadan wanda aka saukar da Alƙur’ani a cikinsa, shiriya ga mutane…” (Al-Baqarah: 185). Wannan ya sa karatunsa a wannan wata ya fi lada da tasiri a zuciya sama da sauran watanni.* *Manzon Allah ﷺ ya kasance yana ƙara yawaita karatun Alƙur’ani a Ramadan, har ma Mala’ika Jibrilu (AS) yana yi masa muraja'a da Alƙur'ani a kowane dare. Wannan yana nuna muhimmancin komawa ga Alƙur’ani domin tsarkake zuciya, da ƙarfafa imani, da neman kusanci da Allah.* *Karatun Alƙur’ani a Ramadan:* • *Yana ƙara haske da nutsuwa a zuciya.* • *Yana ninka lada, domin wata ne na alheri da rahama.* • *Yana taimaka wa mai azumi ya kiyaye harshensa da halayensa.* *Don haka, ya dace mu tsara lokaci a Ramadan domin yawaita karatu da tadabburi da sauraren tafsirai daga bakin malamai, da aiki da Alƙur’ani, domin shi ne babban sakon wannan wata mai alfarma.* _©By Zauren Hikimomin Malaman Sunnah🖋️_
0 Comments 0 Shares 522 Views 0 Reviews
Zoomer Africa https://zoomer.africa