*TSARABAR RAMADAN...!*

Ya kai ɗana… ka zauna ka saurara, domin maganar Ramadan ba wasa ba ce.

Ramadan wata ne da Allah Ya buɗe ƙofofin rahama, Ya rage sharrin shaiɗanu, Ya ɗaga darajar masu ibada. Amma ka sani, ba kowa ne yake cin ribarsa ba sai wanda ya shirya zuciyarsa.

Ramadan ba yunwa ba ce kawai, Idan ka bar abinci amma ka kasa barin gulma da ƙarya! hassada da sabo, to me ka samu? Yunwa da ƙishirwa kawai wai?¿

Ya kai ɗana…
Ramadan kamar bako ne mai daraja! Idan ya zo maka ka girmama shi, Ka tarbe shi da tuba da gyaran niyya, da yanke shawarar barin abin da Allah ba ya so! Domin ba ka da tabbacin za ka sake ganinsa shekara mai zuwa.

Ka sani har ila yau
ɗana…!
Sallah ita ce ginshiƙi, Kada ka yi sakaci da ita!
Alƙur’ani abokin Ramadan ne, ka yi hulɗa da shi ko da aya ɗaya ce a rana!
Ka taimaki talaka, domin addu’arsa na iya zama cetonka! Ka gyara halinka a gida kafin ka nemi lada a masallaci.

Ya kai ɗana…
Ramadan wata makaranta ce, wanda ya fito daga cikinta, amma bai canza ba, to ya rasa babban abu!
Manufa ba wai gama azumin ba ne, a'ah azumin ya gyara ka.

Ka tuna:
Rayuwa gajeriya ce! Ramadan wata dama ce ta karshe ga wasu, kada ka bari ya wuce maka kamar sauran watanni!

Allah Ya sa mu dace, Ya sa mu fita daga Ramadan da zuciya mai tsarki, zunubi gafararre, da suna cikin jerin bayi salihai. 🤲

*Wannan shine sabon account nawa na Facebook please kuyi fallow nawa*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
https://www.facebook.com/share/1E5Qog7ghQ/

*NAGODE*
*TSARABAR RAMADAN...!* Ya kai ɗana… ka zauna ka saurara, domin maganar Ramadan ba wasa ba ce. Ramadan wata ne da Allah Ya buɗe ƙofofin rahama, Ya rage sharrin shaiɗanu, Ya ɗaga darajar masu ibada. Amma ka sani, ba kowa ne yake cin ribarsa ba sai wanda ya shirya zuciyarsa. Ramadan ba yunwa ba ce kawai, Idan ka bar abinci amma ka kasa barin gulma da ƙarya! hassada da sabo, to me ka samu? Yunwa da ƙishirwa kawai wai?¿ Ya kai ɗana… Ramadan kamar bako ne mai daraja! Idan ya zo maka ka girmama shi, Ka tarbe shi da tuba da gyaran niyya, da yanke shawarar barin abin da Allah ba ya so! Domin ba ka da tabbacin za ka sake ganinsa shekara mai zuwa. Ka sani har ila yau ɗana…! Sallah ita ce ginshiƙi, Kada ka yi sakaci da ita! Alƙur’ani abokin Ramadan ne, ka yi hulɗa da shi ko da aya ɗaya ce a rana! Ka taimaki talaka, domin addu’arsa na iya zama cetonka! Ka gyara halinka a gida kafin ka nemi lada a masallaci. Ya kai ɗana… Ramadan wata makaranta ce, wanda ya fito daga cikinta, amma bai canza ba, to ya rasa babban abu! Manufa ba wai gama azumin ba ne, a'ah azumin ya gyara ka. Ka tuna: Rayuwa gajeriya ce! Ramadan wata dama ce ta karshe ga wasu, kada ka bari ya wuce maka kamar sauran watanni! Allah Ya sa mu dace, Ya sa mu fita daga Ramadan da zuciya mai tsarki, zunubi gafararre, da suna cikin jerin bayi salihai. 🤲 *Wannan shine sabon account nawa na Facebook please kuyi fallow nawa* 👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 https://www.facebook.com/share/1E5Qog7ghQ/ *NAGODE*
WWW.FACEBOOK.COM
Mustapha Salisu
Mustapha Salisu. 2,508 likes · 2,978 talking about this. Ya ubangiji Allah kasadamu da alkairin duniya da lahira Ameen🤲🏼
Love
1
0 Commentaires 0 Parts 114 Vue 0 Avis
Zoomer Africa https://zoomer.africa