DUK WANI SHIRME DA RASHIN JI DA ZAKA YI A LOKACIN TASHEN BALAGA, KA KIYAYE JEFA KANKA A CIKIN WADANNAN HALAYEN:

Dan'uwa, ko da kana ganin jinin samartaka yana zafi...

1. Kada ka koyi shaye-shaye:
(Hanya ce ta hauka da kaskanci).

2. Kada Rashin Sallah ya bika:
(Idan ka yanke alaka da Allah, ka yanke alaka da nasara).

3. Kada ka koyi caca:
(Tana talauta rayuwa da kashe zuciyar neman halak).

4. Kada ka jefa kanka cikin Zinace-Zinace
(Bashi ne, kuma tana toshe hasken zuciya).

5. Kada ka zama mai saba wa Iyayenka:(Wannan itace babban musiba. Albarkar iyaye ita ce sirrin daukaka, tsinuwarsu kuma ita ce tushen halaka).

6. Kada ka bi Abokan Banza:
(Duk abin da ke sama, abokan banza ne suke koya su. Idan ka bi su, ka bata rayuwarka).

7.Kada ka bari ka girma baka da Sana'ar Hannu ko 'Skill':
(Rayuwar yanzu ba ta takardu bace kawai. Sana'ar hannu ita ce 'Inshorar' rayuwarka idan aikin ofis ya gagara. Rashin sana'a yana maida namiji bawan wani).

Dan'uwa, akwai kurakuran da suke da matukar wahalar gyarawa a rayuwa bayan mutum ya girma. Wadannan da na lissafo su ne "Ciwan Dajin" rayuwa.

Idan suka bi jikinka, fitar da su sai an sha wuya.
Saboda haka, maganin bari shine: KADA KA FARA.

Abba tarika 10 ✍️
DUK WANI SHIRME DA RASHIN JI DA ZAKA YI A LOKACIN TASHEN BALAGA, KA KIYAYE JEFA KANKA A CIKIN WADANNAN HALAYEN: Dan'uwa, ko da kana ganin jinin samartaka yana zafi... 1. Kada ka koyi shaye-shaye: (Hanya ce ta hauka da kaskanci). 2. Kada Rashin Sallah ya bika: (Idan ka yanke alaka da Allah, ka yanke alaka da nasara). 3. Kada ka koyi caca: (Tana talauta rayuwa da kashe zuciyar neman halak). 4. Kada ka jefa kanka cikin Zinace-Zinace (Bashi ne, kuma tana toshe hasken zuciya). 5. Kada ka zama mai saba wa Iyayenka:(Wannan itace babban musiba. Albarkar iyaye ita ce sirrin daukaka, tsinuwarsu kuma ita ce tushen halaka). 6. Kada ka bi Abokan Banza: (Duk abin da ke sama, abokan banza ne suke koya su. Idan ka bi su, ka bata rayuwarka). 7.Kada ka bari ka girma baka da Sana'ar Hannu ko 'Skill': (Rayuwar yanzu ba ta takardu bace kawai. Sana'ar hannu ita ce 'Inshorar' rayuwarka idan aikin ofis ya gagara. Rashin sana'a yana maida namiji bawan wani). Dan'uwa, akwai kurakuran da suke da matukar wahalar gyarawa a rayuwa bayan mutum ya girma. Wadannan da na lissafo su ne "Ciwan Dajin" rayuwa. Idan suka bi jikinka, fitar da su sai an sha wuya. Saboda haka, maganin bari shine: KADA KA FARA. Abba tarika 10 ✍️
Love
1
0 Comments 0 Shares 142 Views 0 Reviews
Zoomer Africa https://zoomer.africa