MANZON ALLAH YA YI GASKIYA!

Wato in mutum yana kallon yadda lamarin al'ummarmu yake tafiya bisa doron kwaikwayon turawan yamma a kan al'adunsu da aƙidunsu da suka ci karo da musulunci, zai ƙara sakankacewa cewa lallai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama mai gaskiya ne kuma abin gasgatawa. Ya faɗa a cikin hadisi ingantacce cewa: Lallai za ku bi tafarkin waɗanda suka gabace ku ɗani bayan ɗani, kamu bayan kamu, ko da kuwa sun shiga ramin damo ne za ku shiga ku ma. Sahabbai suka ce ya Ma'aikin Allah (kana nufin) Yahudu da Nasara? Yace: to su wa? Bukhari da Muslim suka rawaito shi.
A yau mun wayi gari da kwaikwayon waɗannan mutane ta fuskoki daban-daban, mafi muni shi ne ayyukansu da suka ƙunshi aƙidun ɓata da cin karo da shari'ar Annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama.
Bikin zagayowar ranar haihuwa ya zamo mana ruwan dare, taya su murnar bikin kirsimeti ya zama alama ta nuna son zaman lafiya da sanin yakamata wurin wasu, zuwa bukukuwan murnar sabuwar shekara kuwa yanzu kai ka ce wata alama ce ta wayewa, sannu a hankali tana mamayarmu in da za ka ga wanda ba ka zata ba shi ma ya tafi wannan bukukuwan, ba manya ba yara!

Anya muna hankaltar me hakan ke nufi kuwa? Me muke ƙoƙarin ɗora yaranmu a kai ke nan? Shin duk damar nishaɗi da addininmu ya ba mu ba ta ishe mu ba ne sai mun ƙaro da ta su? Me muke so mu cimma?

🖊Zainab Ja'afar Mahmud
11th Rajab 1447A.H
1st Jan 2026
MANZON ALLAH YA YI GASKIYA! Wato in mutum yana kallon yadda lamarin al'ummarmu yake tafiya bisa doron kwaikwayon turawan yamma a kan al'adunsu da aƙidunsu da suka ci karo da musulunci, zai ƙara sakankacewa cewa lallai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama mai gaskiya ne kuma abin gasgatawa. Ya faɗa a cikin hadisi ingantacce cewa: Lallai za ku bi tafarkin waɗanda suka gabace ku ɗani bayan ɗani, kamu bayan kamu, ko da kuwa sun shiga ramin damo ne za ku shiga ku ma. Sahabbai suka ce ya Ma'aikin Allah (kana nufin) Yahudu da Nasara? Yace: to su wa? Bukhari da Muslim suka rawaito shi. A yau mun wayi gari da kwaikwayon waɗannan mutane ta fuskoki daban-daban, mafi muni shi ne ayyukansu da suka ƙunshi aƙidun ɓata da cin karo da shari'ar Annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama. Bikin zagayowar ranar haihuwa ya zamo mana ruwan dare, taya su murnar bikin kirsimeti ya zama alama ta nuna son zaman lafiya da sanin yakamata wurin wasu, zuwa bukukuwan murnar sabuwar shekara kuwa yanzu kai ka ce wata alama ce ta wayewa, sannu a hankali tana mamayarmu in da za ka ga wanda ba ka zata ba shi ma ya tafi wannan bukukuwan, ba manya ba yara! Anya muna hankaltar me hakan ke nufi kuwa? Me muke ƙoƙarin ɗora yaranmu a kai ke nan? Shin duk damar nishaɗi da addininmu ya ba mu ba ta ishe mu ba ne sai mun ƙaro da ta su? Me muke so mu cimma? 🖊Zainab Ja'afar Mahmud 11th Rajab 1447A.H 1st Jan 2026
0 Comments 0 Shares 467 Views 0 Reviews
Zoomer Africa https://zoomer.africa