https://whatsapp.com/channel/0029Vb7NDqJ3QxRyFqmYYW19/411
https://whatsapp.com/channel/0029Vb7NDqJ3QxRyFqmYYW19/411
WHATSAPP.COM
MALAM AHMAD TIJJANI YUSUF GRNTUM 01: HUKUNCIN MACE TAYI SALLA KAFAFUNTA A WAJE?! : 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓ : Assalamu Alaikum. Malam barka da yau Allah ya qara rufa asiri. Malam shin menene hukuncin sallah da qafafuwa waje ga mace, inajin malamai na cewa babu banbanci ga sallar macce da ta namiji da Manzon Allah (S A W) yace kuyi sallah kamar yanda kukaga inayi, ban saniba ko nayi kuskure toh naga maza basa rufe qafafuwan su, don Allah malam ina son sanin hukuncin sallah da safa shin dole ne ko mustahabbi?? Nagode : 𝐀𝐌𝐒𝐀❗️ : Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh An shar'anta wa mace baliga wacce ba baiwa ba, ta rufe jikin ta baki ɗayansa idan zatayi sallah, sai fuskar ta da tafukan hannayenta ne kaɗai bazata rufe ba. Saboda ita mace 'ya gabaɗayanta al'aurah ce. Idan tayi sallah alhali bata rufe wani sashen jikinta ba kamar qwaurinta ko kafarta ko dukansu ko kuma wani sashen kanta a buɗe, toh sallar ta bata yi ba. Manzon Allah (sallallaahu alaihi wa sallam) yace: "لا يقبل الله صلاة حائض إلا بخمار" رواه أحمد وأهل السنن إلا النسائي بإسناد صحيح. "Allah baya karɓar sallar mace wacce ta fara al'ada har saida khimaar (mayafin rufe kai)" Ahmad da Abu Dawud da Ibn Majah da Tirmizi suka ruwaito shi da isnaadi ingantacce. و لما روى أبو داود عن أم سلمة عن النبي صلى الله عليه و سلم أنها سألت النبي عن المرأة تصلي في درع و خمار بغير إزار فقال: " المرأة عورة" Abu Dawuda ya ruwaito daga Ummu Salamah (radiyallah anha) cewa ta tambayi Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) gameda matar da tayi sallah tana sanye da dir'a (kamar riga) da khimaar (mayafin rufe kai) amma bata sanya Izaar (kamar wando na mata mai rufe tafukan kafar su) ba? Sai Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) yace "Ita Mace Al'aurah ce" Amma ita fuskar mace, abinda yake sunnah shine baza'a rufe ta ba a lokacin yin sallah matuqar babu maza waɗanda ba muharramanta ba a gurin. Mafiya yawan malamai sunce wajibi ne a rufe tafukan kafa, wasu malaman kuma sunce ba wajibi bane rufe su, amma dai mafiya yawan malamai sun tafi akan wajibcin rufe kafafu gabaɗayansu a yayin sallah. Abu Dawuda ya ruwaito daga Ummu Salamah (radiyallahu anha) cewa an tambaye ta akan matar da tayi sallah tana sanye da khimaar (mayafin rufe kai ko kuma karamin hijabin da bai wuce kwankwaso ba) da kuma qamees (Riga)? Sai Ummu Salamah tace: babu laifi a hakan idan dir'a (wando ko doguwar riga) ɗin nata ya rufe tafukan kafafunta. Amma yafi kyau a kowane irin yanayi ta rufe tafukan kafafunta domin tsallake siradin kokwanto. Saboda haka idan mace zata yi sallah ta sanya safa (socks) yin hakan yafi dacewa. WALLAHU A'ALAM https://chat.whatsapp.com/GP69vX9lMSN03HSdD1IJS4?mode=gi_t
Channel • 7.6K followers
likes
Love
2
1 Comments 0 Shares 621 Views 0 Reviews
Zoomer Africa https://zoomer.africa