KUSKURE MAFI GIRMA DA ZA KA YI A ƘOƘARIN NEMAN KUƊI KO KASUWANCI SUNE...


Wannan rubutu ne mai matuƙar muhimmanci wanda zai iya ceto makomarka. Tsaya ka karanta a natse, domin waɗannan kurakuren su suka ruguza jarin miliyoyin matasa a yau:


1. Gaggawar son zama miliyoniya a dare ɗaya: Neman arziki a guje shi yake jefa matasa a caca, damfara, ko kasuwancin banza. Kasuwanci na gaskiya yana buƙatar lokaci da haƙuri; ko sana'ar sayar da wayoyi kake yi, ko harkar sayar da data, ko aikin digital skills, dole ne ka fara daga ƙasa ka gina Trust a wajen mutane. Gaggawa tana kashe albarkar dukiyar.


2. Cinikin babu lissafi ko kasa raba jari da riba: Duk yadda cinikinka ya ke da kyau, idan ba ka san bambancin jarin da ka zuba da kuma ainihin ribar da ta shigo ba, wallahi faɗuwa za ka yi. Yin holewa da kuɗin da kwastoma ya ba ka ba wayewa ba ce; cin mutuncin gumin kanka ne. Jari kamar jini yake ga kasuwanci; idan ka shanye shi, kasuwancin zai mutu.


3. Yin kasuwanci don kawai ka ga wani yana yi: Babban wauta ce ka shiga wata harka don kawai ka ga wani yana samun kuɗi a ciki, ba tare da ka nutsu ka koyi ainihin sirrin aikin da ake buƙata ba. Kowane kasuwanci yana da ƙalubalensa a ɓoye, idan ka shiga a makance ba tare da ilimi ba, asara ce za ta buɗe maka ido.


4. Cire Allah a lissafinka:
Ka ɗauka wayonka, ƙwarewarka, ko kyawun tallan da kake yi su suke kawo maka kwastomomi. Wallahi idan ka manta da cewa Allah ne Mai bayarwa, ya bar ka da dabararka, sai ka ga wanda bai kai ka tsari ko farashi ba yana ciniki, alhali kai kana zaune kana kallon shagonka ko ofishinka babu kowa.


Arziƙi na gaskiya a hankali ake gina shi da riƙon amana, juriya, da kuma cikakken Tawakkali ga Ubangiji. Ka Farka ka gyara lissafinka a yau tun kafin asara ta yi maka gargaɗi mai ɗaci.
ISHAQ ABDULLAHI YUSUF ✍️
KUSKURE MAFI GIRMA DA ZA KA YI A ƘOƘARIN NEMAN KUƊI KO KASUWANCI SUNE... Wannan rubutu ne mai matuƙar muhimmanci wanda zai iya ceto makomarka. Tsaya ka karanta a natse, domin waɗannan kurakuren su suka ruguza jarin miliyoyin matasa a yau: 1. Gaggawar son zama miliyoniya a dare ɗaya: Neman arziki a guje shi yake jefa matasa a caca, damfara, ko kasuwancin banza. Kasuwanci na gaskiya yana buƙatar lokaci da haƙuri; ko sana'ar sayar da wayoyi kake yi, ko harkar sayar da data, ko aikin digital skills, dole ne ka fara daga ƙasa ka gina Trust a wajen mutane. Gaggawa tana kashe albarkar dukiyar. 2. Cinikin babu lissafi ko kasa raba jari da riba: Duk yadda cinikinka ya ke da kyau, idan ba ka san bambancin jarin da ka zuba da kuma ainihin ribar da ta shigo ba, wallahi faɗuwa za ka yi. Yin holewa da kuɗin da kwastoma ya ba ka ba wayewa ba ce; cin mutuncin gumin kanka ne. Jari kamar jini yake ga kasuwanci; idan ka shanye shi, kasuwancin zai mutu. 3. Yin kasuwanci don kawai ka ga wani yana yi: Babban wauta ce ka shiga wata harka don kawai ka ga wani yana samun kuɗi a ciki, ba tare da ka nutsu ka koyi ainihin sirrin aikin da ake buƙata ba. Kowane kasuwanci yana da ƙalubalensa a ɓoye, idan ka shiga a makance ba tare da ilimi ba, asara ce za ta buɗe maka ido. 4. Cire Allah a lissafinka: Ka ɗauka wayonka, ƙwarewarka, ko kyawun tallan da kake yi su suke kawo maka kwastomomi. Wallahi idan ka manta da cewa Allah ne Mai bayarwa, ya bar ka da dabararka, sai ka ga wanda bai kai ka tsari ko farashi ba yana ciniki, alhali kai kana zaune kana kallon shagonka ko ofishinka babu kowa. Arziƙi na gaskiya a hankali ake gina shi da riƙon amana, juriya, da kuma cikakken Tawakkali ga Ubangiji. Ka Farka ka gyara lissafinka a yau tun kafin asara ta yi maka gargaɗi mai ɗaci. ISHAQ ABDULLAHI YUSUF ✍️
0 التعليقات ·0 المشاركات ·397 المشاهدات ·0 التقييمات
Zoomer Africa https://zoomer.africa