• Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya kira ga ʼyan Najeriya su riƙa gode wa Shugaba Tinubu kan ƙoƙarin da ya yi, duba da yanayin da ƙasar ke ciki lokacin da ya hau mulki.

    Ya kuma bayyana ƙwarin gwiwar cewa APC za ta lashe zaɓen 2027.
    Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya kira ga ʼyan Najeriya su riƙa gode wa Shugaba Tinubu kan ƙoƙarin da ya yi, duba da yanayin da ƙasar ke ciki lokacin da ya hau mulki. Ya kuma bayyana ƙwarin gwiwar cewa APC za ta lashe zaɓen 2027.
    likes
    1
    0 Comments 0 Shares 152 Views 0 Reviews
  • 🤲 ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!! 🤲

    SAKON GODIYA, JINJINA DA FATAN ALKHAIRI GA AL'UMMAR KIRU DA KUMA KUDANGORA

    Zan yi amfani da wannan dama domin mika sakon godiya ta musamman da jinjina ga wasu hazikan mutane masu kishin al'umma, bisa jajircewarsu, kwazonsu da kuma kokarinsu na ganin cewa Allah (SWT) Ya tabbatar da aikin kafa FEDERAL UNIVERSITY a wannan yanki namu mai albarka.

    A yau, 11 ga Oktoba, 2026, an gudanar da aikin duba wurin da aka tsara domin gina wannan babbar makaranta ta tarayya a yankinmu na Kiru. Wannan mataki abin farin ciki ne matuka, domin idan Allah Ya tabbatar da wannan aiki, zai bude sabon babi na ci gaba a rayuwar al'ummar wannan yanki.

    Babu shakka, kafa jami'a a wannan yanki zai taimaka wajen bunkasa harkokin ilimi, samar da karin damar karatu ga matasa, habaka tattalin arziki, samar da guraben ayyukan yi da kuma kara darajar yankinmu a idon duniya.

    A bisa wannan gagarumin kokari, ina mika sakon godiya da jinjina ta musamman ga wadannan manyan mutane da masu kishin al'umma:

    1. Mai Girma Minista da tawagarsa, bisa gudunmawarsu da kokarinsu.
    2. Uban Kasa, Hakimin Kiru, bisa rawar da yake takawa wajen ci gaban al'ummar yankin.
    3. Shugaban Karamar Hukumar Kiru (Chairman Kiru Local Government), bisa goyon baya da kokarinsa.
    4. Sarki Salisu Kiru, bisa gudunmawarsa da kishin ci gaban yankin.
    5. Dattawan Kiru (Kiru Elders), bisa shawarwari da gudunmawar da suke bayarwa.
    6. Principal, Coexist Kiru, da sauran dukkan wadanda suka bayar da tasu gudunmawar wajen ganin wannan buri ya fara zama gaskiya.

    Hakika, wannan kokari abin a yaba ne, kuma muna addu'ar Allah Ya saka wa kowa da alheri, Ya kara musu basira da ikon ci gaba da hidimar al'umma.

    Wani abin farin ciki da kuma alfahari shi ne shirin samar da harabar jami'ar guda biyu (TWO CAMPUSES), daya a cikin garin Kiru, dayan kuma a Kudangora. Wannan tsari, idan aka tabbatar da shi, zai ba bangarorin biyu damar cin moriyar wannan gagarumin aikin ci gaba.

    A ganina, ci gaban Kiru da Kudangora ci gaba ne ga daukacin al'ummarmu. Bai kamata mu mayar da wannan dama ta ci gaba tamkar wata gasa tsakanin yankuna ba. Maimakon haka, ya kamata mu hada kai, mu tallafa wa juna, tare da ba da fifiko ga abin da zai amfani al'ummarmu baki daya.

    Jami'a ba ginin makaranta kawai ba ce; ginshiki ce ta ilimi, cigaban tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma gina makoma mai kyau ga 'ya'yanmu da jikokinmu.

    A karshe, muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya tabbatar mana da wannan aiki, Ya saukaka dukkan matakai, Ya ba wadanda suke kokari a kansa ikon kammala shi cikin nasara. Allah Ya sanya wannan jami'a ta zama sanadin daukakar Kiru, Kudangora da daukacin al'ummarmu.

    Allah Ya hada kanmu, Ya kara mana zaman lafiya, Ya kawo mana ci gaba mai dorewa, kuma Ya tabbatar mana da wannan babban buri. AMIN YA RABBAL ALAMIN! 🤲

    KIRU DA KUDANGORA: HADIN KAI DOMIN ILIMI DA CIGABA! 🤝🎓

    ✍️ Ishaq Abdullahi Yusuf
    🤲 ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!! 🤲 SAKON GODIYA, JINJINA DA FATAN ALKHAIRI GA AL'UMMAR KIRU DA KUMA KUDANGORA Zan yi amfani da wannan dama domin mika sakon godiya ta musamman da jinjina ga wasu hazikan mutane masu kishin al'umma, bisa jajircewarsu, kwazonsu da kuma kokarinsu na ganin cewa Allah (SWT) Ya tabbatar da aikin kafa FEDERAL UNIVERSITY a wannan yanki namu mai albarka. A yau, 11 ga Oktoba, 2026, an gudanar da aikin duba wurin da aka tsara domin gina wannan babbar makaranta ta tarayya a yankinmu na Kiru. Wannan mataki abin farin ciki ne matuka, domin idan Allah Ya tabbatar da wannan aiki, zai bude sabon babi na ci gaba a rayuwar al'ummar wannan yanki. Babu shakka, kafa jami'a a wannan yanki zai taimaka wajen bunkasa harkokin ilimi, samar da karin damar karatu ga matasa, habaka tattalin arziki, samar da guraben ayyukan yi da kuma kara darajar yankinmu a idon duniya. A bisa wannan gagarumin kokari, ina mika sakon godiya da jinjina ta musamman ga wadannan manyan mutane da masu kishin al'umma: 1. Mai Girma Minista da tawagarsa, bisa gudunmawarsu da kokarinsu. 2. Uban Kasa, Hakimin Kiru, bisa rawar da yake takawa wajen ci gaban al'ummar yankin. 3. Shugaban Karamar Hukumar Kiru (Chairman Kiru Local Government), bisa goyon baya da kokarinsa. 4. Sarki Salisu Kiru, bisa gudunmawarsa da kishin ci gaban yankin. 5. Dattawan Kiru (Kiru Elders), bisa shawarwari da gudunmawar da suke bayarwa. 6. Principal, Coexist Kiru, da sauran dukkan wadanda suka bayar da tasu gudunmawar wajen ganin wannan buri ya fara zama gaskiya. Hakika, wannan kokari abin a yaba ne, kuma muna addu'ar Allah Ya saka wa kowa da alheri, Ya kara musu basira da ikon ci gaba da hidimar al'umma. Wani abin farin ciki da kuma alfahari shi ne shirin samar da harabar jami'ar guda biyu (TWO CAMPUSES), daya a cikin garin Kiru, dayan kuma a Kudangora. Wannan tsari, idan aka tabbatar da shi, zai ba bangarorin biyu damar cin moriyar wannan gagarumin aikin ci gaba. A ganina, ci gaban Kiru da Kudangora ci gaba ne ga daukacin al'ummarmu. Bai kamata mu mayar da wannan dama ta ci gaba tamkar wata gasa tsakanin yankuna ba. Maimakon haka, ya kamata mu hada kai, mu tallafa wa juna, tare da ba da fifiko ga abin da zai amfani al'ummarmu baki daya. Jami'a ba ginin makaranta kawai ba ce; ginshiki ce ta ilimi, cigaban tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma gina makoma mai kyau ga 'ya'yanmu da jikokinmu. A karshe, muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya tabbatar mana da wannan aiki, Ya saukaka dukkan matakai, Ya ba wadanda suke kokari a kansa ikon kammala shi cikin nasara. Allah Ya sanya wannan jami'a ta zama sanadin daukakar Kiru, Kudangora da daukacin al'ummarmu. Allah Ya hada kanmu, Ya kara mana zaman lafiya, Ya kawo mana ci gaba mai dorewa, kuma Ya tabbatar mana da wannan babban buri. AMIN YA RABBAL ALAMIN! 🤲 KIRU DA KUDANGORA: HADIN KAI DOMIN ILIMI DA CIGABA! 🤝🎓 ✍️ Ishaq Abdullahi Yusuf
    likes
    7
    1 Comments 0 Shares 582 Views 0 Reviews
  • *📌 FADAKARWA TA SAFIYA — ASABAR*

    *Assalamu Alaikum warahmatullah!*

    Yau Asabar ce — wata dama ce sabuwa daga Allah. Ka yi amfani da wannan safiyar domin:

    ✅ Ka tuba daga zunubanka
    ✅ Ka gyara niyyarka da zuciyarka
    ✅ Ka tuna da mutuwa da lahira
    ✅ Ka ziyarci iyaye ko ka kira su
    ✅ Ka taimaki wani da kalma ko da’awa ko sadaka

    🗣️ *“Duk wanda ya fara safiyarsa da istighfari, Allah zai buɗe masa ƙofa na rahama.”*

    *Kada ka bar wannan safiyar ta wuce ba tare da ka ambaci Allah ba!*
    Allah Ya sa mu dace, Ya albarkaci Asabar ɗinmu da dukkan kwanakinmu.
    *Ameen.*
    *📌 FADAKARWA TA SAFIYA — ASABAR* *Assalamu Alaikum warahmatullah!* Yau Asabar ce — wata dama ce sabuwa daga Allah. Ka yi amfani da wannan safiyar domin: ✅ Ka tuba daga zunubanka ✅ Ka gyara niyyarka da zuciyarka ✅ Ka tuna da mutuwa da lahira ✅ Ka ziyarci iyaye ko ka kira su ✅ Ka taimaki wani da kalma ko da’awa ko sadaka 🗣️ *“Duk wanda ya fara safiyarsa da istighfari, Allah zai buɗe masa ƙofa na rahama.”* *Kada ka bar wannan safiyar ta wuce ba tare da ka ambaci Allah ba!* Allah Ya sa mu dace, Ya albarkaci Asabar ɗinmu da dukkan kwanakinmu. *Ameen.*
    likes
    Love
    2
    0 Comments 0 Shares 1K Views 0 Reviews
  • MANZON ALLAH (SAW) "BA A JUYO DA ADDU'A TSAKANIN KIRAN SALLAH DA TAYAR DA IƘAMAH "

    FA'IDA
    WANNAN HADISI YANA KOYA MANA MAHIMMANCIN YIN ADDU'A A TSAKANIN KIRAN SALLAH HAR ZUWA LOKACIN DA ZA A TAYAR DA IƘAMAH
    MANZON ALLAH (SAW) "BA A JUYO DA ADDU'A TSAKANIN KIRAN SALLAH DA TAYAR DA IƘAMAH " FA'IDA WANNAN HADISI YANA KOYA MANA MAHIMMANCIN YIN ADDU'A A TSAKANIN KIRAN SALLAH HAR ZUWA LOKACIN DA ZA A TAYAR DA IƘAMAH
    0 Comments 0 Shares 629 Views 0 Reviews
  • 🌹🌹Manzon Allah S.A.W Yace :"Haqiqa A Cikin Aljannah Akwai Wata Qofa Ana Kiranta Rayyan, Babu Mai Shiga Aljannah Ta Cikinta Sai Masu Yin Azumi A Ranar Alqiyama, Kuma Duk Wanda Ba Su Ba Ba zai Shiga Tare Da Su Ba, Za'a ce:" Ina Masu Yin Azumi ? Sai Su Shige Tanan,Idan Na Qarshe Ya Shige,Sai A Rufe Qofar, Kuma Babu Wanda Zai Sake Shiga Tanan."🌹🌹

    Muslim
    🌹🌹Manzon Allah S.A.W Yace :"Haqiqa A Cikin Aljannah Akwai Wata Qofa Ana Kiranta Rayyan, Babu Mai Shiga Aljannah Ta Cikinta Sai Masu Yin Azumi A Ranar Alqiyama, Kuma Duk Wanda Ba Su Ba Ba zai Shiga Tare Da Su Ba, Za'a ce:" Ina Masu Yin Azumi ? Sai Su Shige Tanan,Idan Na Qarshe Ya Shige,Sai A Rufe Qofar, Kuma Babu Wanda Zai Sake Shiga Tanan."🌹🌹 Muslim
    likes
    Love
    2
    0 Comments 0 Shares 1K Views 0 Reviews
  • 🔲KIRDADON DAREN LAILATUL QADR.🔲

    🌹🌹Manzon Allah S.A.W yace : Ku yi kirdadon daren lailatul qadr a wutiri na goman qarshe a watan ramadan.🌹🌹

    Bukhari da Muslim
    🔲KIRDADON DAREN LAILATUL QADR.🔲 🌹🌹Manzon Allah S.A.W yace : Ku yi kirdadon daren lailatul qadr a wutiri na goman qarshe a watan ramadan.🌹🌹 Bukhari da Muslim
    0 Comments 0 Shares 954 Views 0 Reviews
  • 🌹🌹Manzon Allah S.A.W Yace :"Haqiqa A Cikin Aljannah Akwai Wata Qofa Ana Kiranta Rayyan, Babu Mai Shiga Aljannah Ta Cikinta Sai Masu Yin Azumi A Ranar Alqiyama, Kuma Duk Wanda Ba Su Ba Ba zai Shiga Tare Da Su Ba, Za'a ce:" Ina Masu Yin Azumi ? Sai Su Shige Tanan,Idan Na Qarshe Ya Shige,Sai A Rufe Qofar, Kuma Babu Wanda Zai Sake Shiga Tanan."🌹🌹

    Muslim
    🌹🌹Manzon Allah S.A.W Yace :"Haqiqa A Cikin Aljannah Akwai Wata Qofa Ana Kiranta Rayyan, Babu Mai Shiga Aljannah Ta Cikinta Sai Masu Yin Azumi A Ranar Alqiyama, Kuma Duk Wanda Ba Su Ba Ba zai Shiga Tare Da Su Ba, Za'a ce:" Ina Masu Yin Azumi ? Sai Su Shige Tanan,Idan Na Qarshe Ya Shige,Sai A Rufe Qofar, Kuma Babu Wanda Zai Sake Shiga Tanan."🌹🌹 Muslim
    likes
    Love
    2
    0 Comments 0 Shares 648 Views 0 Reviews
  • 🚀 PI NETWORK NA NUNA KARFIN BULLISH A KASUWA

    Ina matuƙar farin ciki da yadda Pi Network ke ƙara nuna ƙarfi a kasuwar crypto. Duk da cewa wasu projects suna fama da matsaloli, Pi yana ci gaba da nuna alamun ci gaba na dogon lokaci.

    Community da tsarin ecosystem ɗin Pi suna ƙara ƙarfi kullum a hankali.

    ⚠️ MUHIMMIN SANARWA:
    Abin da ake kira GCV (Global Consensus Value) wannan duk yaudarace (scam). Don haka ku guje masa gaba ɗaya, kada ku yarda da duk wanda yake yaɗa wannan labarin.

    📌 Shawara mai sauƙi:
    Ku ci gaba da tara Pi a hankali, ku mai da hankali kan ainihin ci gaban ecosystem ɗin Pi.

    A wasu lokuta mafi kyawun dabara ita ce ka riƙe abin da kake da shi ka jira lokacin sa.

    ✍🏼Alsadiq
    10/03/2026
    🚀 PI NETWORK NA NUNA KARFIN BULLISH A KASUWA Ina matuƙar farin ciki da yadda Pi Network ke ƙara nuna ƙarfi a kasuwar crypto. Duk da cewa wasu projects suna fama da matsaloli, Pi yana ci gaba da nuna alamun ci gaba na dogon lokaci. Community da tsarin ecosystem ɗin Pi suna ƙara ƙarfi kullum a hankali. ⚠️ MUHIMMIN SANARWA: Abin da ake kira GCV (Global Consensus Value) wannan duk yaudarace (scam). Don haka ku guje masa gaba ɗaya, kada ku yarda da duk wanda yake yaɗa wannan labarin. 📌 Shawara mai sauƙi: Ku ci gaba da tara Pi a hankali, ku mai da hankali kan ainihin ci gaban ecosystem ɗin Pi. A wasu lokuta mafi kyawun dabara ita ce ka riƙe abin da kake da shi ka jira lokacin sa. ✍🏼Alsadiq 10/03/2026
    likes
    Love
    2
    0 Comments 0 Shares 2K Views 0 Reviews
  • *🕊️JUMA’A MAI ALBARKA..🕌🕊️*

    *Wannan rana ce ta musamman da ta fi girma a wurin Allah Ta’ala…*

    *Ya ku muminai Idan aka yi kiran sallah a ranar Juma’a ku nufi zuwa wajen ambaton Allah ku daina kasuwanci Wannan ne mafi alheri a gare ku, idan kun sani*
    *(Suratul Jumu’ah: 9)*

    *Me yasa Juma’a ta ke da girma? Ranar Juma’a ita ce shugabar dukkan ranaku kuma mafi girma a wurin Allah fiye da Idul Adha da Idul Fitr Tana ɗauke da manyan alamu guda 5*

    *1️⃣ A wannan rana Allah (SWT) ya halicci Annabi Adamu (AS)*
    *2️⃣ A wannan rana ne aka saukar da shi duniya*
    *3️⃣ A wannan rana ne aka karɓi ransa*
    *4️⃣ A cikinta akwai wani lokaci na musamman da duk abin da bawa ya roƙa in ba haram ba za a ba shi*
    *5️⃣ Kuma ranar Alƙiyama za ta auku ne a Juma’a*

    *Ibn Majah ya ruwaito cewa babu wani mala’ika ko sama ko ƙasa ko iska ko dutse ko teku da ba ya tsoron wannan rana mai girma*

    *Mu yawaita salati ga Annabi ﷺ mu kuma nemi gafara da rahamar Allah a wannan rana mai albarka Juma’a Mubarak 🙏🏻*
    *🕊️JUMA’A MAI ALBARKA..🕌🕊️* *Wannan rana ce ta musamman da ta fi girma a wurin Allah Ta’ala…* *Ya ku muminai Idan aka yi kiran sallah a ranar Juma’a ku nufi zuwa wajen ambaton Allah ku daina kasuwanci Wannan ne mafi alheri a gare ku, idan kun sani* *(Suratul Jumu’ah: 9)* *Me yasa Juma’a ta ke da girma? Ranar Juma’a ita ce shugabar dukkan ranaku kuma mafi girma a wurin Allah fiye da Idul Adha da Idul Fitr Tana ɗauke da manyan alamu guda 5* *1️⃣ A wannan rana Allah (SWT) ya halicci Annabi Adamu (AS)* *2️⃣ A wannan rana ne aka saukar da shi duniya* *3️⃣ A wannan rana ne aka karɓi ransa* *4️⃣ A cikinta akwai wani lokaci na musamman da duk abin da bawa ya roƙa in ba haram ba za a ba shi* *5️⃣ Kuma ranar Alƙiyama za ta auku ne a Juma’a* *Ibn Majah ya ruwaito cewa babu wani mala’ika ko sama ko ƙasa ko iska ko dutse ko teku da ba ya tsoron wannan rana mai girma* *Mu yawaita salati ga Annabi ﷺ mu kuma nemi gafara da rahamar Allah a wannan rana mai albarka Juma’a Mubarak 🙏🏻*
    Love
    likes
    3
    1 Comments 0 Shares 623 Views 0 Reviews
  • *ME CECE SALLAH*

    Sallah na nufin addu'a.
    Amma a shari'ance ibada ce ma'abociyar karatu da ayyuka kebabbu, da ake fara ta da kabbara a kuma rufe ta da sallama, sallah ita ce rukuni na biyu a cikin Addinin Musulunci bayan kalmar shahada, wato (ASH'HADU AN LA ILAHA ILALLAHU WA ASH'HADU ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH) sai ita.
    kuma ita ce kashin bayan addini, saboda girmanta da matsayinta Allah bai aiko mala’ika da ita ba sai Allah Madaukakin Sarki Ya kirawo Annabi (SAW) a daren Isra’i da Mi’iraji ya bashi ita. Yana daga girman sallah ambatonta da Allah Madaukakin Sarki Yayi sau hamsin da takwas (58) a cikin Alkur’ani, kamar inda yake cewa:
    {وَأَقِيمُوا الصَّلَوةَ} [البقرة: 43]
    Ma'ana: "Ku tsaida sallah"
    {قُلْ لِعِبَادِيَ الَّذِينَ آمَنُوا يُقِيمُوا الصَّلَوةَ}[إبراهيم: 31]
    Ma'ana: "Ka fada (Ya Muhammad S.A.W) ga bayina da suka yi imani su tsaida sallah".
    Da sauran wurare a cikin Alqur'ani da dama.

    Annabi (SAW) yana cewa: “Bainar rajuli wabainal kufri tarkus salati” (Rawahu Muslim).
    Ma’ana: “Tsakanin mutum da kafirci shine barin sallah”.
    Kuma ana umartar karamin yaro da yin Sallah tun yana dan shekara bakwai, kuma in ya kai shekara goma a doke shi in ya ki yi.

    Sallah bata yiwuwa sai da alwala.

    *🕌IRSHADUL UMMAH WHATSAPP, 07060902016*

    _Bin Muhammad✍️_
    *ME CECE SALLAH* Sallah na nufin addu'a. Amma a shari'ance ibada ce ma'abociyar karatu da ayyuka kebabbu, da ake fara ta da kabbara a kuma rufe ta da sallama, sallah ita ce rukuni na biyu a cikin Addinin Musulunci bayan kalmar shahada, wato (ASH'HADU AN LA ILAHA ILALLAHU WA ASH'HADU ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH) sai ita. kuma ita ce kashin bayan addini, saboda girmanta da matsayinta Allah bai aiko mala’ika da ita ba sai Allah Madaukakin Sarki Ya kirawo Annabi (SAW) a daren Isra’i da Mi’iraji ya bashi ita. Yana daga girman sallah ambatonta da Allah Madaukakin Sarki Yayi sau hamsin da takwas (58) a cikin Alkur’ani, kamar inda yake cewa: {وَأَقِيمُوا الصَّلَوةَ} [البقرة: 43] Ma'ana: "Ku tsaida sallah" {قُلْ لِعِبَادِيَ الَّذِينَ آمَنُوا يُقِيمُوا الصَّلَوةَ}[إبراهيم: 31] Ma'ana: "Ka fada (Ya Muhammad S.A.W) ga bayina da suka yi imani su tsaida sallah". Da sauran wurare a cikin Alqur'ani da dama. Annabi (SAW) yana cewa: “Bainar rajuli wabainal kufri tarkus salati” (Rawahu Muslim). Ma’ana: “Tsakanin mutum da kafirci shine barin sallah”. Kuma ana umartar karamin yaro da yin Sallah tun yana dan shekara bakwai, kuma in ya kai shekara goma a doke shi in ya ki yi. Sallah bata yiwuwa sai da alwala. *🕌IRSHADUL UMMAH WHATSAPP, 07060902016* _Bin Muhammad✍️_
    Love
    1
    0 Comments 0 Shares 732 Views 0 Reviews
  • *ASSALAMU ALAIKUM BARKAN MU DA SAFIYAR YAU [LAHADI]*

    *NASIHAR MU TA YAU*
    ```Daga Matashin kirki ake Samun Dattijon Arziki, idan kuma kaga tsohon Banza to yaron banza ne ya girma, Kada ka yadda ka shiga cikin mutanen banza wadanda Allah baya kallo da idon rahama.

    *Ya Allah kasa mu kasance Alkhairi ga kowa ka nisanta mu da mummunan aiki kowane iri ne, Amin ya hayyu ya Qayyum.🤲*
    *ASSALAMU ALAIKUM BARKAN MU DA SAFIYAR YAU [LAHADI]* *NASIHAR MU TA YAU* ```Daga Matashin kirki ake Samun Dattijon Arziki, idan kuma kaga tsohon Banza to yaron banza ne ya girma, Kada ka yadda ka shiga cikin mutanen banza wadanda Allah baya kallo da idon rahama. *Ya Allah kasa mu kasance Alkhairi ga kowa ka nisanta mu da mummunan aiki kowane iri ne, Amin ya hayyu ya Qayyum.🤲*
    0 Comments 0 Shares 563 Views 0 Reviews
  • MANZON ALLAH YA YI GASKIYA!

    Wato in mutum yana kallon yadda lamarin al'ummarmu yake tafiya bisa doron kwaikwayon turawan yamma a kan al'adunsu da aƙidunsu da suka ci karo da musulunci, zai ƙara sakankacewa cewa lallai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama mai gaskiya ne kuma abin gasgatawa. Ya faɗa a cikin hadisi ingantacce cewa: Lallai za ku bi tafarkin waɗanda suka gabace ku ɗani bayan ɗani, kamu bayan kamu, ko da kuwa sun shiga ramin damo ne za ku shiga ku ma. Sahabbai suka ce ya Ma'aikin Allah (kana nufin) Yahudu da Nasara? Yace: to su wa? Bukhari da Muslim suka rawaito shi.
    A yau mun wayi gari da kwaikwayon waɗannan mutane ta fuskoki daban-daban, mafi muni shi ne ayyukansu da suka ƙunshi aƙidun ɓata da cin karo da shari'ar Annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama.
    Bikin zagayowar ranar haihuwa ya zamo mana ruwan dare, taya su murnar bikin kirsimeti ya zama alama ta nuna son zaman lafiya da sanin yakamata wurin wasu, zuwa bukukuwan murnar sabuwar shekara kuwa yanzu kai ka ce wata alama ce ta wayewa, sannu a hankali tana mamayarmu in da za ka ga wanda ba ka zata ba shi ma ya tafi wannan bukukuwan, ba manya ba yara!

    Anya muna hankaltar me hakan ke nufi kuwa? Me muke ƙoƙarin ɗora yaranmu a kai ke nan? Shin duk damar nishaɗi da addininmu ya ba mu ba ta ishe mu ba ne sai mun ƙaro da ta su? Me muke so mu cimma?

    🖊Zainab Ja'afar Mahmud
    11th Rajab 1447A.H
    1st Jan 2026
    MANZON ALLAH YA YI GASKIYA! Wato in mutum yana kallon yadda lamarin al'ummarmu yake tafiya bisa doron kwaikwayon turawan yamma a kan al'adunsu da aƙidunsu da suka ci karo da musulunci, zai ƙara sakankacewa cewa lallai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama mai gaskiya ne kuma abin gasgatawa. Ya faɗa a cikin hadisi ingantacce cewa: Lallai za ku bi tafarkin waɗanda suka gabace ku ɗani bayan ɗani, kamu bayan kamu, ko da kuwa sun shiga ramin damo ne za ku shiga ku ma. Sahabbai suka ce ya Ma'aikin Allah (kana nufin) Yahudu da Nasara? Yace: to su wa? Bukhari da Muslim suka rawaito shi. A yau mun wayi gari da kwaikwayon waɗannan mutane ta fuskoki daban-daban, mafi muni shi ne ayyukansu da suka ƙunshi aƙidun ɓata da cin karo da shari'ar Annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama. Bikin zagayowar ranar haihuwa ya zamo mana ruwan dare, taya su murnar bikin kirsimeti ya zama alama ta nuna son zaman lafiya da sanin yakamata wurin wasu, zuwa bukukuwan murnar sabuwar shekara kuwa yanzu kai ka ce wata alama ce ta wayewa, sannu a hankali tana mamayarmu in da za ka ga wanda ba ka zata ba shi ma ya tafi wannan bukukuwan, ba manya ba yara! Anya muna hankaltar me hakan ke nufi kuwa? Me muke ƙoƙarin ɗora yaranmu a kai ke nan? Shin duk damar nishaɗi da addininmu ya ba mu ba ta ishe mu ba ne sai mun ƙaro da ta su? Me muke so mu cimma? 🖊Zainab Ja'afar Mahmud 11th Rajab 1447A.H 1st Jan 2026
    likes
    1
    0 Comments 0 Shares 596 Views 0 Reviews
More Results
Zoomer Africa https://zoomer.africa