*MAFARIN TAFIYA*
(Yaƙin Ma'aurata)
Ina yawan samun koke-koken sabbin ma'aurata game da yawan saɓani ko rashin jituwa da suke samu da abokan rayuwarsu a farkon zama.
Abin da nake so masu shirin aure da ma'aurata su fahimta:
Wannan saɓanin da yake yawan faruwa a shekarar farko na aure, ba yana nufin auren ba zai yuwu ba ne, kuma ba yana nufin ma'auratan sun gaza ba ne, kusan dole ne a samu hakan ga mutane biyu da suka fara rayuwa tare a inuwa ɗaya, alhali sun fito daga rassa daban-daban; wataƙila al'adunsu ya banbanta, yanayin inda suka taso, tarbiyyarsu, ko ma yarensu.
Kuma duk lokacin da mutum biyu suka zauna tare ko da kuwa abota ce ko ƙawance to dole sai an yi haƙuri da juna.
Duk da cewa lokacin neman aure ana tattaunawa domin a fahimci juna, amma maganar gaskiya:
Baza ku san juna cikakken sani ba, sai kun zauna tare.
Saboda haka kafin ku kai ga matakin fahimtar juna, dole ne duka ɓangarorin biyu ku rungumi haƙuri, ku bi komai sannu sannu a hankali.
Nasihata gare ku itace:
Ku kasance masu hikmah:
Musamman namiji, tunda kai ne jagora, ka san yadda zaka tafiyar da saɓani cikin lumana da hikmah ba tare da zargi ko tashin hankali ba.
Don Allah maza:
Ku kasance masu haƙuri da ƙura-kuren da kuke gani, kuyi gyara cikin nasiha da taushin harshe.
Mata:
Ku kasance masu buɗaɗɗiyar zuciya wajen karɓan gyara, namijin da yake so ki samu babban matsayi a zuciyarsa, shi ne wanda zai dinga miki gyara yana ɗaura ki a hanya, domin idan ƙura-kurenki suka yi yawa ba tare da gyara ba matsayinki zai iya zagwanyewa a zuciyarshi.
Kuma ku sani:
Waɗanda kuke gani sunyi nasara a aurensu, ba wai don basa saɓani ba ne; a'a sun kasance masu juriya ne gurin fuskantar matsalolinsu, masu ƙoƙarin fahimtar juna, da kuma kyautata wa juna zato.
Don Allah, ku ɗauki wannan shekarar ta farko a matsayin "Shekarar haƙuri" kada kuyi saurin yanke wa juna hukunci a cikinta, saboda muhimmancin haƙuri a zaman aure ya sanya bayan anyi aure (a cikin al'ummar Hausawa) kullum dangin ango da na amarya addu'ar su ita ce Allah ya bada zaman haƙuri, saboda haka matuƙar al'amari bai taɓa imani da lafiyar jiki ba ko afkawa haramun to haƙuri da addu'a da kawar da kai zasu magance dukkan matsaloli.
Billah alaikum:
Ku kyautata niyyoyinku, ku zauna da juna da zuciya ɗaya.
Allah ya ƙarfafe ku, ya sanya albarka a cikin zamantakewarku, ya kare ku daga ko wace irin fitna.
*Oum Hanan* 🌹