🌙 Ramadan 2026 🌙
Ya Allah…
Ga mu a gabanka, muna shiga watan da Ka ɗaukaka, wata da Ka saukar da Al-Qur’ani a cikinsa, wata da Ka buɗe ƙofofin rahama, Ka rufe ƙofofin wuta.
Ya Rabbana, ba da ƙarfarmu muka iso ba, da rahamarka muka iso.
Da yawa daga cikin waɗanda muka yi Ramadan tare da su bara. ba su kai wannan shekarar ba. Ka nuna mana ni’imarka, kada Ka hana mu cikakkiyar moriyarta.
Ya Allah, Ka sa wannan watan ya zama sauyi a rayuwarmu.
Ka tsarkake zuƙatanmu daga riya da girman kai da hassada.
Ka tsare harshenmu daga ƙarya da gulma.
Ka tsare idanunmu da kunnuwanmu daga haram.
Ya Allah, Ka ba mu ikon azumi da tsayuwar dare cikin cikakken imani da neman lada, bisa koyarwar AnnabinKa Muhammad ﷺ.
Ka sa Al-Qur’ani ya zama abokin rayuwarmu, hasken kabarinmu, mai cetonmu ranar tashin ƙiyama.
Ka ba mu dacewa mu riski Lailatul Qadr, Ka rubuta mu cikin ‘yantattu daga wuta.
Ya Allah, Ka gyara mana iyalanmu, Ka haɗa zukatanmu bisa alheri, Ka wadata talakawanmu, Ka aurar da matasanmu da zawarawanmu, Ka ba marasa lafiya lafiya, Ka yaye damuwar masu damuwa.
Ya Allah, idan wannan shi ne Ramadan na ƙarshe a rayuwarmu. Ka sa ya zama mafi alheri a gare mu.
Idan za Ka ƙara mana tsawon rai, Ka sa mu kai Ramadan mai zuwa cikin ƙarin shiriya da tsoronKa.
🤲 Amin Ya Rabbal ‘Alamin.
*Kuyi sharing domin Yan uwa masu albarka suma su amfana.*
_*WhatsApp Channel*_
https://whatsapp.com/channel/0029VaOoKxLEVccM1YHNJy1Y
*_Facebook_*
https://www.facebook.com/profile.php?id=100085881057085
_Ɗan Uwanku Amusulunci_
_*Mustapha Salisu ✍🏼*_