• *Muhimmancin Karatun Alƙur’ani a Watan Ramadan.*

    *Ramadan wata ne da aka saukar da Alƙur’ani a cikinsa, kamar yadda Allah Ya ce:*
    *“Watan Ramadan wanda aka saukar da Alƙur’ani a cikinsa, shiriya ga mutane…” (Al-Baqarah: 185). Wannan ya sa karatunsa a wannan wata ya fi lada da tasiri a zuciya sama da sauran watanni.*

    *Manzon Allah ﷺ ya kasance yana ƙara yawaita karatun Alƙur’ani a Ramadan, har ma Mala’ika Jibrilu (AS) yana yi masa muraja'a da Alƙur'ani a kowane dare. Wannan yana nuna muhimmancin komawa ga Alƙur’ani domin tsarkake zuciya, da ƙarfafa imani, da neman kusanci da Allah.*

    *Karatun Alƙur’ani a Ramadan:*
    • *Yana ƙara haske da nutsuwa a zuciya.*
    • *Yana ninka lada, domin wata ne na alheri da rahama.*
    • *Yana taimaka wa mai azumi ya kiyaye harshensa da halayensa.*

    *Don haka, ya dace mu tsara lokaci a Ramadan domin yawaita karatu da tadabburi da sauraren tafsirai daga bakin malamai, da aiki da Alƙur’ani, domin shi ne babban sakon wannan wata mai alfarma.*

    _©By Zauren Hikimomin Malaman Sunnah🖋️_
    *Muhimmancin Karatun Alƙur’ani a Watan Ramadan.* *Ramadan wata ne da aka saukar da Alƙur’ani a cikinsa, kamar yadda Allah Ya ce:* *“Watan Ramadan wanda aka saukar da Alƙur’ani a cikinsa, shiriya ga mutane…” (Al-Baqarah: 185). Wannan ya sa karatunsa a wannan wata ya fi lada da tasiri a zuciya sama da sauran watanni.* *Manzon Allah ﷺ ya kasance yana ƙara yawaita karatun Alƙur’ani a Ramadan, har ma Mala’ika Jibrilu (AS) yana yi masa muraja'a da Alƙur'ani a kowane dare. Wannan yana nuna muhimmancin komawa ga Alƙur’ani domin tsarkake zuciya, da ƙarfafa imani, da neman kusanci da Allah.* *Karatun Alƙur’ani a Ramadan:* • *Yana ƙara haske da nutsuwa a zuciya.* • *Yana ninka lada, domin wata ne na alheri da rahama.* • *Yana taimaka wa mai azumi ya kiyaye harshensa da halayensa.* *Don haka, ya dace mu tsara lokaci a Ramadan domin yawaita karatu da tadabburi da sauraren tafsirai daga bakin malamai, da aiki da Alƙur’ani, domin shi ne babban sakon wannan wata mai alfarma.* _©By Zauren Hikimomin Malaman Sunnah🖋️_
    0 التعليقات 0 المشاركات 523 المشاهدات 0 التقييمات
  • *Addu’ar Kariya da Tarbiya ga ƴarki.*

    *“Allahumma ihdiha wahdi biha, waj‘alha min ‘ibadikaṣ-ṣaliḥat.*
    *Allahumma ṭahhir qalbaha, wa ḥaṣṣin farjaha, wa ṣrif ‘anha su’a wal-faḥsha.*
    *Allahumma ḥabbib* *ilaihal-īmān wa zayyinhu fī qalbiha, wa karrih* *ilaihal-kufra wal-fusūqa wal-‘iṣyān.*
    *Allahumma aj‘alha barratan biwālidayha, maḥfūẓatan bi ‘aynīk allati lā tanām.”*
    *اللَّهُمَّ اهْدِهَا وَاهْدِ بِهَا، وَاجْعَلْهَا مِنْ عِبَادِكَ الصَّالِحَاتِ.*
    *اللَّهُمَّ طَهِّرْ قَلْبَهَا، وَحَصِّنْ فَرْجَهَا، وَاصْرِفْ عَنْهَا السُّوءَ وَالْفَحْشَاءَ.*
    *اللَّهُمَّ حَبِّبْ إِلَيْهَا الإِيمَانَ وَزَيِّنْهُ فِي قَلْبِهَا، وَكَرِّهْ إِلَيْهَا الْكُفْرَ وَالْفُسُوقَ وَالْعِصْيَانَ.*
    *اللَّهُمَّ اجْعَلْهَا بَرَّةً بِوَالِدَيْهَا، مَحْفُوظَةً بِعَيْنِكَ الَّتِي لَا تَنَامُ.*

    *Ma’ana:*
    *Ya Allah Ka shiryar da ita, Ka sanya ta cikin bayinka na ƙwarai.*
    *Ka tsarkake zuciyarta, Ka kare mutuncinta, Ka nisantar da ita daga sharri da alfasha.*
    *Ka sanya ta so imani, Ka ƙawata shi a zuciyarta, Ka sa ta ƙi saɓo da zunubi.*
    *Ka sanya ta m
    *Addu’ar Kariya da Tarbiya ga ƴarki.* *“Allahumma ihdiha wahdi biha, waj‘alha min ‘ibadikaṣ-ṣaliḥat.* *Allahumma ṭahhir qalbaha, wa ḥaṣṣin farjaha, wa ṣrif ‘anha su’a wal-faḥsha.* *Allahumma ḥabbib* *ilaihal-īmān wa zayyinhu fī qalbiha, wa karrih* *ilaihal-kufra wal-fusūqa wal-‘iṣyān.* *Allahumma aj‘alha barratan biwālidayha, maḥfūẓatan bi ‘aynīk allati lā tanām.”* *اللَّهُمَّ اهْدِهَا وَاهْدِ بِهَا، وَاجْعَلْهَا مِنْ عِبَادِكَ الصَّالِحَاتِ.* *اللَّهُمَّ طَهِّرْ قَلْبَهَا، وَحَصِّنْ فَرْجَهَا، وَاصْرِفْ عَنْهَا السُّوءَ وَالْفَحْشَاءَ.* *اللَّهُمَّ حَبِّبْ إِلَيْهَا الإِيمَانَ وَزَيِّنْهُ فِي قَلْبِهَا، وَكَرِّهْ إِلَيْهَا الْكُفْرَ وَالْفُسُوقَ وَالْعِصْيَانَ.* *اللَّهُمَّ اجْعَلْهَا بَرَّةً بِوَالِدَيْهَا، مَحْفُوظَةً بِعَيْنِكَ الَّتِي لَا تَنَامُ.* *Ma’ana:* *Ya Allah Ka shiryar da ita, Ka sanya ta cikin bayinka na ƙwarai.* *Ka tsarkake zuciyarta, Ka kare mutuncinta, Ka nisantar da ita daga sharri da alfasha.* *Ka sanya ta so imani, Ka ƙawata shi a zuciyarta, Ka sa ta ƙi saɓo da zunubi.* *Ka sanya ta m
    0 التعليقات 0 المشاركات 127 المشاهدات 0 التقييمات
  • *Idan kana son ka tsare ƴaƴanka daga lalacewa a zamanin nan, da rayuwa mara ma’ana, ka shuka musu waɗannan ginshiƙai guda huɗu tun suna ƙanana:*

    *1. Tarbiyyar jajircewa da neman na kai.*
    *Ka koya musu cewa duk abin da ake buri, ana samunsa ne da ƙoƙari da juriya. Idan ana son ilimi, a dage da karatu. Idan ana son wadata, a jure wahalar nema. Idan ana son ‘yanci da daraja, a tashi tsaye a bi hanyarsa.*

    *Rashin wannan tarbiyya ne ya haifar da raunin zuciya a cikin al’umma, har wasu suka koma masu jiran a tallafa musu maimakon su tashi su nemi nasu. Sai ka ga lafiyayyen mutum, amma ya kashe himmarsa, yana jiran wani ɗan’uwa mai kuɗi, ko gwamnati ko wani mai hali ya warware masa matsalolinsa ba tare da ya motsa ba. Wannan ba halin ɗa mai tarbiyya ba ne.*

    *2. Tarbiyyar godiya da rama alheri.*
    *Ka gina su a kan godiya ga duk wanda ya yi musu alheri, da kuma ƙoƙarin rama alheri da alheri. Idan ka shuka musu wannan dabi’a, kai ne za ka fi kowa amfana da ita. Domin za su riƙa tuna alherinka, su kula da kai lokacin
    *Idan kana son ka tsare ƴaƴanka daga lalacewa a zamanin nan, da rayuwa mara ma’ana, ka shuka musu waɗannan ginshiƙai guda huɗu tun suna ƙanana:* *1. Tarbiyyar jajircewa da neman na kai.* *Ka koya musu cewa duk abin da ake buri, ana samunsa ne da ƙoƙari da juriya. Idan ana son ilimi, a dage da karatu. Idan ana son wadata, a jure wahalar nema. Idan ana son ‘yanci da daraja, a tashi tsaye a bi hanyarsa.* *Rashin wannan tarbiyya ne ya haifar da raunin zuciya a cikin al’umma, har wasu suka koma masu jiran a tallafa musu maimakon su tashi su nemi nasu. Sai ka ga lafiyayyen mutum, amma ya kashe himmarsa, yana jiran wani ɗan’uwa mai kuɗi, ko gwamnati ko wani mai hali ya warware masa matsalolinsa ba tare da ya motsa ba. Wannan ba halin ɗa mai tarbiyya ba ne.* *2. Tarbiyyar godiya da rama alheri.* *Ka gina su a kan godiya ga duk wanda ya yi musu alheri, da kuma ƙoƙarin rama alheri da alheri. Idan ka shuka musu wannan dabi’a, kai ne za ka fi kowa amfana da ita. Domin za su riƙa tuna alherinka, su kula da kai lokacin
    0 التعليقات 0 المشاركات 476 المشاهدات 0 التقييمات
  • *Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Lallai ALLAH (ﷻ) Ya ce: “Dukkan aikin ɗan-adam na shi ne (kansa yayi ma), amma banda azumi, lallai shi na wa ne, kuma ni zanyi sakamako a kansa...” [Bukhari:1904, Muslim: 1151]*

    *Ibnu Qudamah Almaqdisy (Rahimahullah) Ya ce: “Ka sani cewa shi azumi yana da wani matsayi na musamman wanda waninsa bashi da shi, shi ne jingina shi zuwa ga ALLAH (ﷻ) wajen da yake cewa a cikin Hadith Qudsiy “Azumi na wa ne nine zan bayar da ladansa.” Wannan jinginawar kaɗai ta isa ɗaukaka/daraja.” [Minhajul Qaasideen p: 49]*

    *Hadith ƙudusy ko Hadith Rabbany ko Hadith ilahy maganar ALLAH ne wanda Manzon ALLAH (ﷺ) Yake ruwaitowa daga gare shi, kuma wannan hadisin ya nuna girma da falalar azumi akan sauran ibadu.*

    _©By Abdullahi Aliyu Bonza 🖋️_
    *Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Lallai ALLAH (ﷻ) Ya ce: “Dukkan aikin ɗan-adam na shi ne (kansa yayi ma), amma banda azumi, lallai shi na wa ne, kuma ni zanyi sakamako a kansa...” [Bukhari:1904, Muslim: 1151]* *Ibnu Qudamah Almaqdisy (Rahimahullah) Ya ce: “Ka sani cewa shi azumi yana da wani matsayi na musamman wanda waninsa bashi da shi, shi ne jingina shi zuwa ga ALLAH (ﷻ) wajen da yake cewa a cikin Hadith Qudsiy “Azumi na wa ne nine zan bayar da ladansa.” Wannan jinginawar kaɗai ta isa ɗaukaka/daraja.” [Minhajul Qaasideen p: 49]* *Hadith ƙudusy ko Hadith Rabbany ko Hadith ilahy maganar ALLAH ne wanda Manzon ALLAH (ﷺ) Yake ruwaitowa daga gare shi, kuma wannan hadisin ya nuna girma da falalar azumi akan sauran ibadu.* _©By Abdullahi Aliyu Bonza 🖋️_
    0 التعليقات 0 المشاركات 511 المشاهدات 0 التقييمات
  • *JIHADI BIYU A WATAN RAMADAN!!!*

    *Ibnu Rajab Al-hanbaliy (Rahimahullah) Ya ce: “Lallai ka sani shi Mumini Jihadi biyu suna haɗuwa masa a watan Ramadan:*

    *1● Jihadi da rana na yin Azumi.*
    *2● Jihadi da dare na yin Ƙiyamullaili.*

    *Duk wanda ya haɗa waɗannan jihadi guda biyun kuma ya basu haƙƙoƙinsu, yayi haƙuri a kansu, toh ya cika ladansa a wajen ALLAH ba tare da iyakancewa ba.” [Laɗa'if Alma'aarif: 171]*

    _©By Taskar Hadisan Manzon Allah🖋️_
    *JIHADI BIYU A WATAN RAMADAN!!!* *Ibnu Rajab Al-hanbaliy (Rahimahullah) Ya ce: “Lallai ka sani shi Mumini Jihadi biyu suna haɗuwa masa a watan Ramadan:* *1● Jihadi da rana na yin Azumi.* *2● Jihadi da dare na yin Ƙiyamullaili.* *Duk wanda ya haɗa waɗannan jihadi guda biyun kuma ya basu haƙƙoƙinsu, yayi haƙuri a kansu, toh ya cika ladansa a wajen ALLAH ba tare da iyakancewa ba.” [Laɗa'if Alma'aarif: 171]* _©By Taskar Hadisan Manzon Allah🖋️_
    0 التعليقات 0 المشاركات 98 المشاهدات 0 التقييمات
  • *Hanyoyi 5 na samun qarin lada a azumi da bayan azumi.*

    *1. Sayen tankin ruwa a kai unguwar da ke buqatan ruwa.*

    *2. Ɗinka normal hijabs ko na sallah a bada sadakan su ga masu buqata.*

    *3. Saye da raba Qur'anai ko litattatafan addu'oi ga masu buqata*

    *4. Rabama 'yan uwa iyaye dan abin da za su sayi kayan shayi ko a tura musu kayan shayin ko dan kudin da zasu sayi abin buqata na shan ruwa.*

    *5. Ɗin kama marayun 'yan uwan ko na makwabta ko masu marayuwan kayan sallah.*

    _©By Darajar 'Ya Mace a Musulunci🖋️_
    *Hanyoyi 5 na samun qarin lada a azumi da bayan azumi.* *1. Sayen tankin ruwa a kai unguwar da ke buqatan ruwa.* *2. Ɗinka normal hijabs ko na sallah a bada sadakan su ga masu buqata.* *3. Saye da raba Qur'anai ko litattatafan addu'oi ga masu buqata* *4. Rabama 'yan uwa iyaye dan abin da za su sayi kayan shayi ko a tura musu kayan shayin ko dan kudin da zasu sayi abin buqata na shan ruwa.* *5. Ɗin kama marayun 'yan uwan ko na makwabta ko masu marayuwan kayan sallah.* _©By Darajar 'Ya Mace a Musulunci🖋️_
    0 التعليقات 0 المشاركات 132 المشاهدات 0 التقييمات
  • *MAFITA 5 GA WANDA AURENSA*
    *YA KUSA DA MAFITA 5 GA WANDA*
    *BAYI DA AURE (MACE KO NA MIJI)*

    *1) Duk wanda Aurensa ya kusa, mace ko na miji, to akwai buƙatan ya samu ishesh-shen lafiya ta fiskan cin Abinci mai kyau, Idan na mijine ya yawaita cin nama da kankana especially lokacin kwanciya, ko da na kwana uku ne kafin Aurensa, idan kuma macene akwai buƙatan ta yawaita ƙoshi da kuma kankana kokuma gwanda.*

    *2) Kada ka yarda har Aurenka yazo dab baka yiwa kanka gyara wajen ibada ba, dole saika gyara imaninka sosai, sallah akan lokaci, tsayuwan dare koda Raka'ah biyu ne, kuma kayi riƙo da Istigfari yadda ya kamata.*

    *3) Kada Aurenka ya kusa amma mahaifiyarka bata jin daɗinka, wallahi idan kaga jarrabawa bayan Aurenka to akwai abinda kayiwa iyayenka especially uwa idan tana raye, lalle ka nemi yardansu, ma'ana kayi Aure suna so kayi.*

    *4) Idan Aurenki ko Aurenka ya kusa, dole ka koyi haƙuri, da kuma gani da kaucar da kai, ita kuma mace dolene ta koyi iya magana da kuma girki yadda ya kamata, da ƙwarƙwasa a cik
    *MAFITA 5 GA WANDA AURENSA* *YA KUSA DA MAFITA 5 GA WANDA* *BAYI DA AURE (MACE KO NA MIJI)* *1) Duk wanda Aurensa ya kusa, mace ko na miji, to akwai buƙatan ya samu ishesh-shen lafiya ta fiskan cin Abinci mai kyau, Idan na mijine ya yawaita cin nama da kankana especially lokacin kwanciya, ko da na kwana uku ne kafin Aurensa, idan kuma macene akwai buƙatan ta yawaita ƙoshi da kuma kankana kokuma gwanda.* *2) Kada ka yarda har Aurenka yazo dab baka yiwa kanka gyara wajen ibada ba, dole saika gyara imaninka sosai, sallah akan lokaci, tsayuwan dare koda Raka'ah biyu ne, kuma kayi riƙo da Istigfari yadda ya kamata.* *3) Kada Aurenka ya kusa amma mahaifiyarka bata jin daɗinka, wallahi idan kaga jarrabawa bayan Aurenka to akwai abinda kayiwa iyayenka especially uwa idan tana raye, lalle ka nemi yardansu, ma'ana kayi Aure suna so kayi.* *4) Idan Aurenki ko Aurenka ya kusa, dole ka koyi haƙuri, da kuma gani da kaucar da kai, ita kuma mace dolene ta koyi iya magana da kuma girki yadda ya kamata, da ƙwarƙwasa a cik
    0 التعليقات 0 المشاركات 516 المشاهدات 0 التقييمات
  • *Kada ka taɓa wasa da Sallah akan lokacinta.*

    Wallahi, ya fi maka alheri ka rasa komai a cikin wannan duniya fiye da ka bar Sallah guda ɗaya ta wuce maka akan lokacinta.

    Jinkirta Sallah ba tare da uzuri ba babban zunubi ne wanda zai iya ja mutum zuwa wutar Jahannama cikin sauƙi.

    Allah Ya tsare mu daga sakaci da Sallah, Ya sa mu kasance cikin masu tsayawa da ita a kan lokaci.
    *Kada ka taɓa wasa da Sallah akan lokacinta.* Wallahi, ya fi maka alheri ka rasa komai a cikin wannan duniya fiye da ka bar Sallah guda ɗaya ta wuce maka akan lokacinta. Jinkirta Sallah ba tare da uzuri ba babban zunubi ne wanda zai iya ja mutum zuwa wutar Jahannama cikin sauƙi. Allah Ya tsare mu daga sakaci da Sallah, Ya sa mu kasance cikin masu tsayawa da ita a kan lokaci.
    0 التعليقات 0 المشاركات 564 المشاهدات 0 التقييمات
  • Rashin sanin abin da gobe ke ɗauke da shi, shi ne ke sa wasu farin ciki da mummunar ƙaddara ga rayuwar wani.

    `Mustapha Salisu` ✍🏼
    Rashin sanin abin da gobe ke ɗauke da shi, shi ne ke sa wasu farin ciki da mummunar ƙaddara ga rayuwar wani. `Mustapha Salisu` ✍🏼
    0 التعليقات 0 المشاركات 158 المشاهدات 0 التقييمات
  • *Mu yi sadaka domin Allah*☝️

    Ya ku bayin Allah!
    Ku sani—sadaka tana tsarkake dukiya, tana tsarkake zuciya, tana jawo albarka, tana kawar da bala’i, tana ƙarfafa rayuwa. Duk wanda ya yi ta yin sadaka domin Allah, Allah Zai sa masa lada har abada, ba tare da rage dukiyarsa ba.

    Ku tambayi kanku...
    *“Shin ina bayar da sadaka domin neman yardar Allah, ko saboda mutane su yaba mini ?*
    _Shin zuciyata tana son riko da dukiya, ko kuma tana neman girmama Allah ne ?_

    Wallahi, sadaka da niyyar duniya kawai ba zata tsarkake zuciya ba😭 Amma sadaka ta gaskiya domin Allah tana kawo tsira a duniya da lahira.

    Allah Maɗaukakin Sarki Yana cewa

    > لَن تَنَالُوا الْبِرَّ حَتَّىٰ تُنفِقُوا مِمَّا تُحِبُّونَ ۚ وَمَا تُنفِقُوا مِن شَيْءٍ فَإِنَّ اللَّهَ بِهِ عَلِيمٌ

    Ba za ku kai ga alheri ba har sai kun ciyar da abin da kuke so. Kuma abin da kuka ciyar, lallai Allah Yana sane da shi.

    `Mudage da kokarin taimakawa.`

    Wanda bai samu damar taimakawa ba, Allah Ya ba shi ikon taimakawa.

    *Account Number:* 7013349737
    *Account Name:* Mustapha Salisu
    *Bank Name:* SmartCash

    Allah Ubangiji Ya saka da alheri, Ya ba da iko da yalwar arziki. Ameen. 🤲🏼
    *Mu yi sadaka domin Allah*☝️ Ya ku bayin Allah! Ku sani—sadaka tana tsarkake dukiya, tana tsarkake zuciya, tana jawo albarka, tana kawar da bala’i, tana ƙarfafa rayuwa. Duk wanda ya yi ta yin sadaka domin Allah, Allah Zai sa masa lada har abada, ba tare da rage dukiyarsa ba. Ku tambayi kanku... *“Shin ina bayar da sadaka domin neman yardar Allah, ko saboda mutane su yaba mini ?* _Shin zuciyata tana son riko da dukiya, ko kuma tana neman girmama Allah ne ?_ Wallahi, sadaka da niyyar duniya kawai ba zata tsarkake zuciya ba😭 Amma sadaka ta gaskiya domin Allah tana kawo tsira a duniya da lahira. Allah Maɗaukakin Sarki Yana cewa > لَن تَنَالُوا الْبِرَّ حَتَّىٰ تُنفِقُوا مِمَّا تُحِبُّونَ ۚ وَمَا تُنفِقُوا مِن شَيْءٍ فَإِنَّ اللَّهَ بِهِ عَلِيمٌ Ba za ku kai ga alheri ba har sai kun ciyar da abin da kuke so. Kuma abin da kuka ciyar, lallai Allah Yana sane da shi. `Mudage da kokarin taimakawa.` Wanda bai samu damar taimakawa ba, Allah Ya ba shi ikon taimakawa. *Account Number:* 7013349737 *Account Name:* Mustapha Salisu *Bank Name:* SmartCash Allah Ubangiji Ya saka da alheri, Ya ba da iko da yalwar arziki. Ameen. 🤲🏼
    Love
    1
    0 التعليقات 0 المشاركات 156 المشاهدات 0 التقييمات
Zoomer Africa https://zoomer.africa